Home Labaru Za Mu Kafa Cibiyar Horar Da Ma’Aikata —Abba Gida-Gida

Za Mu Kafa Cibiyar Horar Da Ma’Aikata —Abba Gida-Gida

292
0

Zababben Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf,
ya ce gwamnatin sa za ta himmatu wajen gyara ma’aikatun
gwamnati a wani yunkuri na karfafa tsarin samar da ayyuka
masu inganci.

Abba Gida-Gida ya ce kamar yadda ya ke a cikin tsarin su, za su kafa Cibiyar Horar da Ma’aikatan Gwamnati domin dacewa da mafi kyawun ayyuka na duniya.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Zababben Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.

Abba Gida-Gida, ya taya ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kan su da ke jihar murnar zagayowar Ranar Ma’aikata ta shekara ta 2023.

Ya ce ma’aikata su ne jigon samar da shugabanci nagari a duk wani tsarin dimokuradiyya, don haka sun cancanci a yaba masu bisa sadaukarwar da su ke yi wajen gudanar da aikin su.

Leave a Reply