Home Labaru Za Mu Duba Buƙatun Ƙungiyar Ƙwadago – Tinubu

Za Mu Duba Buƙatun Ƙungiyar Ƙwadago – Tinubu

319
0

Gwamnatin tarayya ta ce za ta yi nazari a kan bukatun
kungiyar kwadago ta TUC, a kokarin dakile yajin aikin da
kungiyoyin kwadago ke barazanar shiga a ranar Laraba
sakamakon cire tallafin man fetur.

Daya daga cikin mahimman bukatun kungiyoyin kwadagon dai shi ne karin mafi karancin albashi.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan wani taro da wakilan kungiyar, mai magana da yawun gwamnati Dele lake ya ce tattaunawar ta yi tasiri kuma su na samun ci-gaba, amma kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC ba ta cikin tattaunawar.

Mista Alake, ya ce da yawa daga cikin bukatun ba wasu abubuwan da za a iya yi ba ne, amma dole ne a yi nazari a kan su tukuna.

Mataki na gaba shi ne, tawagar sa ta gabatar da bukatun kungiyar TUC ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma daya daga cikin bukatun shi ne daga wa ma’aikata kafa a kan haraji.

Dele Alake ya ce za a cigaba da taron a ranar Talata domin bangarorin biyu su duba alfanu da kuma yiwuwar abubuwan da aka gabatar wa gwamnati.

Leave a Reply