Home Labarai Za A Ci Gaba Da Biyan Ma’aikata Ƙarin Albashin Wucin Gadi

Za A Ci Gaba Da Biyan Ma’aikata Ƙarin Albashin Wucin Gadi

126
0
Mohammed Idris
Mohammed Idris

Gwmanatin tarayya ta ce za ta ci gaba da bai wa ma’aikatan ƙasar ƙarin albashin wucin gadi da ta fara biya

ministan yaɗa labarai ya ce wa’adin mafi ƙarancin albashi da aka yi a shekarar 2019 ya ƙare ne 8 ga watan Afrilun 2024.

Sai dai ministan bai bayyana adadin kuɗin da gwamnatin ke biya a matsayin albashin wucin gadin ba,

To a baya gwamnatin ta ce za ta riƙa biyan ma’aikatan ƙarin naira 35,000 a kan albashinsu kowane wata har na tsawon wata shida.

A ranar juma’a ne dai ƙungiyoyin ƙwadogon ƙasar suka ce za su tsunduma yajin aiki daga gobe Litinin,

kasancewar wa’adin ranar da suka bai wa gwamnati na amincewa da mafi ƙarancin albashi ya wuce ba tare da cimma matsaya ba.

Gwamnatin ta ce amince da biyan naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan , to amma haɗakar ƙungiyoyin ƙwadagon sun yi watsi da ƙari,

inda suka buƙaci gwamnati ta biya raira 494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.

Leave a Reply