‘yansandan jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar biyu daga cikin ɗaliban nan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jami’ar ta Osare.
Rundunar ta bayyana kisan daliban a matsayin abin takaici, ta kuma sha alwashin tabbatar da ceto sauran ɗaliban da maharan ke ci gaba da garkuwa da su.
watan Mayu ne maharan suka sace ɗaliban bayan da suka yi wa jami’ar ta su dirar mikiya a lokacin da suke tsaka da karatun fara jarabawa.