Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Mutum 58 Daga Hannun Masu Garkuwa A...

‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Mutum 58 Daga Hannun Masu Garkuwa A Abuja

105
0

Rundunar ‘yan sanda ta birnin tarayya Abuja, ta ce ta ceto
wasu mutane 58 da aka yi garkuwa da su.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan SP Josephine Adeh ta fitar,MUTUM 58

GARKUWA

ta ce an ceto mutanen ne daga dajin Udulu da ke Karamar Hukumar Gegu ta Jihar Kogi, wanda ke da iyaka da Dajin Sardauna na Jihar Nasarawa.

SP Josephine Adeh, ta ce akwai kuma wasu da aka ceto daga wasu sansanonin masu garkuwa da mutanen da aka gano a wasu wurare da ke Abuja.

Ta ce lokacin da barayin su ka ga jami’an tsaro a karkashin jagorancin ‘yan sanda sai su ka soma harbin su, lamarin da ya janyo aka fara musayar wuta.

SP Josephine Adeh ta kara da cewa, lokacin aikin ceton, daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su mai suna Tama Jonathan ya rasu sakamakon raunukan da ya samu, inda ya mutu a wurin nan take.

Leave a Reply