Home Home ‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 17 Kan Zargin Aikata Miyagun Laifuka A...

‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 17 Kan Zargin Aikata Miyagun Laifuka A Zamfara

1
0

Jami’an ‘yan sanda, sun ce sun kama mutane 17 bisa zargin laifuffuka daban-daban ciki har da tashe-tashen hankula bayan zaɓe da fashin daji da satar shanu da kuma sara-suka a jihar Zamfara.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar SP Mohammed Shehu, ya ce jami’an su sun yi kamen ne a sassa daban-daban na jihar Zamfara, tare da ƙwato muhimman kayayyaki daga hannun waɗanda ake zargi.

Rundunar ‘yan sandan, ta ce daga cikin mutanen da ta kama har da wani fitaccen ɗan fashin daji da ya addabi jihar mai suna Sulaiman Balarabe.

Bayan kama wanda ake zargin ne, ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa ya na da hannu a hare-hare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara CP Kolo Yusuf, ya yaba wa al’ummar jihar bisa haɗin kan da su ke ba jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukan su.