Home Home Yan Sanda Sun Kama Matar Da Ta Binne Jaririn Da Ta Haifa...

Yan Sanda Sun Kama Matar Da Ta Binne Jaririn Da Ta Haifa A Jigawa

69
0
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa, ta ce jami’an ta sun kama wata mata mai suna Balaraba Shehu da ke ƙauyen Tsurma a ƙaramar hukumar Kiyawa, bisa zargin binne sabon jaririn da ta haifa a ban-ɗaki.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa, ta ce jami’an ta sun kama wata mata mai suna Balaraba Shehu da ke ƙauyen Tsurma a ƙaramar hukumar Kiyawa, bisa zargin binne sabon jaririn da ta haifa a ban-ɗaki.

Yayin da ya ke tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce sakamakon bayanan sirrin da rundunar su ta samu ne ya kai su ga gano matar tare da tono jaririn.

Ya ce bayan ta haihu ne ta shiga ban-ɗaki ta haƙa rami kusa da Masai ta binne jaririn, inda an bayan tono shi ne aka garzaya da shi babban asibitin Dutse likitoci su ka tabbatar da cewa ya rasu.

DSP Shiisu Adam, ya ce matar ta sanar da su cewa ta samu cikin ne ba ta hanyar aure ba, ta kuma bayyana wani saurayin ta mai suna Ahmadu Sale da aka fi sani da Dan kwairo ya yi mata cikin,.

Tuni dai matar mai shekaru 30 tare da saurayin nata mai shekaru 25 su na hannun jami’an ‘yan sanda.