Home Home ‘Yan Sanda Sun Gano Gidan Sayar Da Jarirai A Nasarawa

‘Yan Sanda Sun Gano Gidan Sayar Da Jarirai A Nasarawa

49
0
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Nasarawa, ta ce ta gano gidan da ake zargin ana saida jarirai a karamar hukumar Karu, inda ta ce ta ceto mata shida da jariri ɗan wata shida a gidan.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Nasarawa, ta ce ta gano gidan da ake zargin ana saida jarirai a karamar hukumar Karu, inda ta ce ta ceto mata shida da jariri ɗan wata shida a gidan.

A wata sanarwar da ya fitar, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan yankinDSP Ramhan Nansel, ya ce da misalin 2 na rana su ka kai samame bayan samun wasu bayanan sirri.

Ya ce ana basaja da gidan ne a matsayin gidan kula da marayu, sai dai bincike ya gano cewa ana garkuwa da kananan yara ana yi masu ciki sannan a saida jariran da su ka haifa.

Tuni dai an kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata wannan mugunyar aika-aika.