Home Labarai ‘Yan Sanda 3 Sun Mutu A Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa...

‘Yan Sanda 3 Sun Mutu A Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Wani Sanata A Nijeriya

321
0

Wasu ‘yan sanda sun gamu da ajalin su, sakamakon harin da ‘yan bindiga su ka kai ma wani dan majalisar dattawa Sanata Ifeanyi Ubah mai wakiltar mazabar Anambra ta Kudu.

‘Yan bindigar, sun kai wa ayarin sanatan harin ne a kauyen Enugwu-Ukwu da ke karamar hukumar Njikoka ta jihar Anambra.

Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun yi wa ayarin Sanata Uba kwanton bauna ne, inda su ka bude masu wuta har suka kashe ‘yan sandan da ba a kai ga tantance adadin su ba.

Wata majiya ta ce, tun da farko ‘yan sandan sun tunkari ‘yan bindigar, inda su ka yi musayar wuta amma duk da haka uku daga cikin su sun mutu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Tochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba a tantance adadin wadanda su ka mutu ba.

Leave a Reply