Home Labaru Yan Najeriya 500 Sun Rasa Ayyukansu A Ƙasar Daular Larabawa

Yan Najeriya 500 Sun Rasa Ayyukansu A Ƙasar Daular Larabawa

20
0
UAE - Nigeria

Rahotanni sun tabbatar da cewa Fiye da ƴan Najeriya 500 ne suka rasa ayyukansu a ƙasar Daular Larabawa bayan da aka dakatar da bayarwa da kuma sabunta bizar aiki ga ƴan Najeriya a ƙasar.

Kafar yada labarai ta Punch ta ruwaito cewa da yawan waɗanda lamarin ya shafa sun dawo gida Najeriya, yayinda ɗaruruwansu kuma ke ci gaba jiran tsammannin ko gwamnatin ƙasar za ta sauya matakin da ta dauka.

Jakadan kasar Daular Larabawan a Najeriya Dr Fahad AI Taffaq, ya ce babu wata sanarwa kan bayar da izinin aiki ga ƴan Najeriyar da ke zaune suna aiki a ƙasarsa.

Taffaq, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabar hukumar da ke kula da ƴan Najeriya a ƙasashen waje Abike Dabiri-Erewa, a ofishin jakadancin kasar dake nan Abuja a watan Agusta, ya shaida mata cewa shi ma a kafafen yaɗa labarai ya ji labarin haramcin, inda ya jaddada cewa kasarsa ba ta sanya takunkumi a kan kowace ƙasa ba.”