Home Labaru Yan Majalisa 18 Sun Amince Da Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara

Yan Majalisa 18 Sun Amince Da Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara

71
0

Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara, ta jefa kuria’r amincewa da tsige Mataimakin Gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau daga muƙamin sa da gagarumin rinjaye.

Yayin wani zama da su ka yi, ‘yan majalisa 18 daga cikin 22 ne su ka amince da ɗaukar matakin, yayin da ɗaya tak ya ki amincewa.

‘Yan majalisar, sun kuma nemi Alƙalin Alƙalai na jihar Zamfara Mai Shari’a Kulu Aliyu ya kafa kwamatin da zai binciki Mahdi bisa zargin saɓa sashe na 190 da 193 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

Dangantaka tsakanin mataimakin gwamnan da uban gidan sa Matawalle dai ta yi tsami ne, tun lokacin ya gwamnan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, amma Mahdi ya cigaba da zama a jam’iyyar PDP.