Home Labarai ‘Yan Bindigan Da Su Ka Sace ‘Yan Ɗaurin Aure Sun Buƙaci A Biya...

‘Yan Bindigan Da Su Ka Sace ‘Yan Ɗaurin Aure Sun Buƙaci A Biya Naira Miliyan 145

41
0

‘Yan bindigar da su ka sace ‘yan ɗaurin aure a hanyar Sokoto zuwa Gusau, sun buƙaci a biya naira miliyan 145 a matsayin kuɗin fansar su, wato naira miliyan 5 kenan a kan kowane mutum daya.

Kakakin Kungiyar matafiyan Ashiru Zurmi, ya ce mutane 20 sun kufce daga hannun ‘yan bindigar a lokacin da su ke shiga da su cikin daji.

Ya Mota ce ta lalace a Tureta Makanike ya zo ya gyara ta, amma ba a wuce mintuna 40 ‘yan bindigar su ka afka wa motar tsakanin Bakura daga Tureta.

Ashiru Zurmi yay i zargin cewa, akwai waɗanda su ka sanar da ‘yan bindigar labarin waɗannan matafiya.