Home Labarai ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 4 Sun Sace 150 A Zamfara

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 4 Sun Sace 150 A Zamfara

77
0
43723b427bcc2b2392cf259309420c86
43723b427bcc2b2392cf259309420c86

’Yan fashin daji sun kashe mutane hudu suka yi garkuwa da wasu 150, ciki har da jarirai a wani kauye da ke Karamar Hukumar Kauran Namoda.

A ranar Lahadi ne ’yan fashin dajin suka kai harin inda suka yi wannan aika-aika a kauyen Dan Isa da ke da tazarar kilomita 14 daga Gusau.

’Yan fashin dajin sun yi wannan danyen aiki a Dan Isa ne kimanin mako guda da suka sako mutum 46 da suka sace a kauyen Dogon Kade bayan karbar kudin fansa Naira miliyan 21.

Wani magidanci a kauyen Dan Isa ya tabbatar da cewa  ’yan fashin dajin sun yi awon gaba da matar sa a yayin harin da suka shafe kimanin awa shida suna cin Karen su babu babbaka,

tun daga misalin karfe uku na ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa ’yan fashin daji sun zo ne a kan babura kimanin 150 kowanne da mutane uku a kan sa, suna harbi kan mai uwa da wabi.

Leave a Reply