Home Home ‘Yan Bindiga Na Neman N500m Kan Kwamishinar Hukumar Kidaya

‘Yan Bindiga Na Neman N500m Kan Kwamishinar Hukumar Kidaya

1
0

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wata Kwamishinar kidaya ta Hukumar Kidaya ta Kasa Misis Gloria Izonfuo a Jihar Bayelsa.

Maharan, sun bukaci a ba su Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansa kafin su saki kwamishinar, wadda su ka yi garkuwa da ita tare da ma’aikatan ta guda biyu.

An dai sace Misis Gloria nea hanyarta ta zuwa  yankin Brass da kejihar Bayelsa daga birnin Fatakwal na jihar Rivers, tare da direban ta da dan aikin ta kamar yadda kakakin ‘yan sanda ta Jihar Rivers Grace Iringe-Koko ta tabbatar.

Grace Iringe-Koko, ta ce tuni kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya tura runduna ta musamman domin ceto mutanen.