Home Labaru Yakin Sudan Darasi Ne Ga Najeriya —Nscia

Yakin Sudan Darasi Ne Ga Najeriya —Nscia

237
0

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya, ta
jaddada muhimmancin da ke akwai ga Nijeriya da ta dauki
darashi daga yakin da ya barke a kassar Sudan.

Ta ce abin da ke faruwa a kasar Sudan, jan hankali ne ga shugabannin Nijeriya su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a kasar nan.

Wata Sanarwa da Daraktan Mulki na Majalisar Zubairu Haruna Usman-Ugwu ya fitar, ta ce mai hankali ya kan dauki izina daga abin da ya faru da wani tun kafin ya same shi ne.

Zubairu Haruna ya ce lokacin siyasa ya wuce, don haka wajibi ne shugabanni da sauran masu fada-a-ji a Nijeriya su dage wajen ganin tabbatuwar kasar nan a dunkule tare da kawo ci- gaba.

Majalisar kolin, ta kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta tura rundunar samar da zaman lafiya zuwa Sudan, domin hana rikicin yaduwar da za ta wargaza zaman lafiya a daukacin yankin Sahel.

Leave a Reply