Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya yi alkawarin samar wa jihar Zamfara karin tallafi a kasafin kudin shekara ta 2019, don samun kudin kara gina jihar da samar da ababen more rayuwa da za su inganta rayuwar al’ummar jihar.
Karanta Wannan: Kishin Kasa: Za Mu Ba ‘Yan Jam’iyyun Adawa Mukamai A Majalisa – Gbajabiamila
Femi Gbajabiamila ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wata ziyara a jihar ta yini guda domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan hanyoyin da za a bi wajen magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
A lokacin ziyarar, Gbajabiamila ya bada gudunmawar kayan abinci ga ‘yan gudun hijira, kuma ya yi alkwarin cewa majalisar tarayya za ta yi iya bakin kokarin ta wajen ganin cewa, an tallafa wa jihar musamman ta hanyar kasafin kudi domin gudanar da aikin ci-gaba da za su farfado da rayuwar al’umma.
Gwamnan jihar ta Zamfara Bello Matawalle ya yi alkwarin ba majalisar hadin kai, domin ganin an samu saukin matsalolin da ake fama da shi a cyankin, sannan ya ce makonni kadan bayan hawan sa mulkin jihar, ya fara tattaunawa da ‘yan bindiga da kuma jami’an sa kai a kan magance matsalar.
Idan
dai ba a mantaba, gwamnatin tarayya ta sha bullo da matakan yaki da matsala ta
tsaro a jihar ta Zamfara, amma lamarin ya ci tura duk da matakan tura sojoji da
ake yia jihar.