Home Labaru Yaki Da Rashawa: Hukumar EFCC Ta Sake Gurfanar Da Fani Kayode,...

Yaki Da Rashawa: Hukumar EFCC Ta Sake Gurfanar Da Fani Kayode, Esther Nnedi Da Wasu

137
0

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC, ta sake gurfanar da tsohuwar ministar kudi, Nnenadi Esther Usman da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode kan damfarar wasu makuden kudade.

Bayan haka kuma hukumar ta kama wani tsohon shugaban ALGON mai suna Yusuf Danjuma, da wani kamfani mai suna Joint-Trust Dimensions Nigeria Limited.

Ana zargin su da laifuka 17 da suka hada da hadin kai wurin yin cuta da kuma adana kudi ba bisa ka’ida ba da suka kai naira biliyan daya da rabi.

Mai shari’a Daniel Osiagor na babban kotun tarayya da ke zama a Ikoyi ta jihar Legas ne ke kan shari’ar.