Home Labaru Yaki Da Dabi’un Cin Zarafin Mata A Najeriya Da Yadda Kwalliya Ke...

Yaki Da Dabi’un Cin Zarafin Mata A Najeriya Da Yadda Kwalliya Ke Biyan Kudin Sabulu

81
0
WhatsApp Image 2024 12 17 at 5.57.37 PM
WhatsApp Image 2024 12 17 at 5.57.37 PM

Ranar 25 ga watan Nuwabar kowace Shekara ce majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar gangamin yaki da cin zarafin mata da ‘ya’ya mata ta duniya.

Ranar an ware ta ne domin wayar da kan al’umma muhimmancin kare ‘ya’ya mata daga cin zarafin su da kuma daukar matakan da suka dace, Taken ranar ta bana shi ne “Hangen nesa dangane da Mata a nan gaba”.

A wannan makon ne aka yi makon kare mata daga cin zarafin su, wakiliyar mu ta tattauna da wasu mata kan irin cin zarafin da suka fuskanta.

Malama Ladidi daga karamar hukumar Chukun a jihar Kaduna ta bayyana yadda kishiyar mahaifiyar ta hana ta karatu ta mata auren dole, ita kuwa Malama Jummai daga karamar hukumar Kagarko bayyana yadda talla ya lalata mata rayu ne har ta dauko abin kunya, yayin da Malama Shatu daga karamar hukumar Lere ta bayyana yadda aikin gida ya sa maigida da babban dan sa suka mayar da ita matar su da kuma yadda ta fuskanci kyara daga uwargida, ita ma Maryam Adamu ta koka ne da yadda ta fuskanci kyara daga mahaifin ta da baya son ‘ya’ya mata duk da kasancewa ita kadai ce mace a tsakanin ‘ya’ya biyar a gidan su, wannan dalili ya sa ta bar gida ta shiga yawon duniya, daga karshe Kezia Iliya ta fadi irin cin zarafin da da fuskanta a wurin mahaifin ta da kishiyar mahaifiyar ta bayan kishiyar ta hana mahaifiyar ta zaman gidan ta kuma asirce mahaifin ta daga karshe dai ta gudu ta koma wurin kanin mahaifin ta.

Dukkan su sun jankalin al’umma dangane da illar cin zarafin ‘ya’ya mata sai suka bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su yi abinda ya dace.

Malaman addini ma ba a bar su a baya ba a bangaren bada gudumawa wajen yaki da cin zarafin mata, Malam Abdulhayyu Musa Thabit Malamin addinin musulunci ne a jihar Kaduna ya ce musulunci tun fil’azal ya daraja ‘ya mace ya kuma kare mata mutunci. Malam ya ce addinance haramun ne cin zarafin ‘ya ce ta kowace hanya.


Shi ma a nasa bangaren Pastor Iliya Auta ya nuna yadda addinin kirista ya daraja ‘ya mace ya ce ko da ALLAH ya samar da Hauwa’u daga hakarkarin annabi Adamu yace masa ne ga abokiyar zama da zata taimaka masa ya samar masa amma ba baiwa ba, dan haka ya gargadi al’umma game da illar cin zarafin mace domin ita baiwar ALLAH ce kuma duk wanda ya ci zarafin ta ya sani ubangiji ya tanadar masa azaba mai tsanani.

Leave a Reply