Home Home Yadda Ma’aikatan Banki Suka Kashe Matar Kwastomansu A Jihar Ogun

Yadda Ma’aikatan Banki Suka Kashe Matar Kwastomansu A Jihar Ogun

101
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Ogun, ta kama wasu ma’aikatan bankin bada lamuni na Micro Finance hudu bisa laifin kashe wata matar abokin huldar su, lokacin da su ke kokarin karbar bashin da mijin ta ya karba.

Matar mai suna Vivian Omo, an zargi daya daga cikin ma’aikatan bankin ne mai suna Ajibulu ya ture ta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ta.

Wata majiya ta ce, ma’aikatan bankin da ke da ofishi a garin Ifo a karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun, sun afka gidan mutumin ne domin neman a ya biya bashin da ya karba, amma Matar ta shaida masu cewa Mijin ta baya gida.

Amsar da Matar ta ba ma’aikatan bankin ce ba ta yi masu dadi ba, inda nan take su ka fara tattara kayayyakin alatun da ke gidan zuwa ofishin su, amma marigayiyar ta hana su kwashe mata kaya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce lokacin da marigayiyar ke takaddama da ma’aikatan bankin sai daya daga cikin su mai suna Ajibulu ya ture ta nan take ta fadi a sume, don haka aka garzaya da ita asibitin da ke kusa domin ceto rayuwar ta, sai dai Likitan asibitin ya bayyana cewa ta mutu.

Leave a Reply