Home Home Yadda Jami’an Tsaro Suka Tsare Peter Obi A London

Yadda Jami’an Tsaro Suka Tsare Peter Obi A London

1
0
Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, ya ce jami’ai sun tsare, tare da hantarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peter Obi a birnin London.

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, ya ce jami’ai sun tsare, tare da hantarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peter Obi a birnin London.

Mai magana da yawun kwamitin Diran Onifade ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewa lamarin ya faru ne a filin jirgin sama na Heathrow da ke London.

Bayanai sun nuna cewa, bayan saukar Peter Obi a filin jirgin na Heathrow da ke London, jami’an tsaro sun je wurin shi lokacin da ya ke kan layin tantancewa, tare da miƙa ma shi wata takarda da ke ƙunshe da umurnin tsarewa, sannan su ka buƙaci ya fita daga layi.

Diran Onifande, ya ce jami’an sun yi wa Peter Obi tambayoyi na tsawon lokaci, wanda abu ne da ba a saba ganin ya faru ga wani mutum da ya kwashe sama da shekaru 10 ya na rayuwa a ƙasar ba.