Home Labaru Yadda Jama’a Suka Kashe Barawon Babur A Ofishin ’Yan Sanda

Yadda Jama’a Suka Kashe Barawon Babur A Ofishin ’Yan Sanda

1
0

Wasu fusatattun matasa sun afka ofishin ‘yan sanda, inda su
ka kwato wani matashi su ka kashe shi nan take, bisa zargin yi
wa kanin sa yankan rago a garin Maigana da ke Karamar
Hukumar Soba ta Jihar Kaduna.

Ana dai zargin matashin da aka kashe ne da lafin sace babur din kanin sa da aka ce ya yi wa yankan rago a kauyen Hayin Ice.

Wani jami’in dan sanda da ya bukaci a sakaya sunan sa ya tabbatar wa manema labarai cewa, a gaban sa fusattattun matasan su ka aika wanda ake zargin barzahu.

Ya ce mutanen da su ka kewaye ofishin su dauke da makamai da duwatsu su na ihun cewa sai an fito da shi ba za su kirgu ba, don haka ganin babu yadda su ka iya dole su ka fito da shi su ka mika shi, inda a nan su ka fara saran shi kafin daga bisani su ka cinna ma shi wuta su ka babbake shi.

Kokarin jin ta bakin kakakin ‘yan sanda na Jihar Kaduna domin ta bakin sa a kan lamarin ya ci tura.