Home Labarai Yadda Hukumar NDLEA Ta Kama Kwalaben Kurkura 26,600 A Kano

Yadda Hukumar NDLEA Ta Kama Kwalaben Kurkura 26,600 A Kano

116
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA reshen jihar Kano, ta kama kwalaben Akurkura dubu 26 da 600 a jihar.

NDLEA, ta kama wani Qasim Ademola a hanyar Zaria zuwa Kano a daidai gadar Tamburawa, wanda dan asalin karamar hukumar Akinyele ne ta jihar Oyo, sannan bayan gudanar da bincike hukumar ta kama wasu mutane uku da ke harƙallar maganin Kurkura.

Hukumar NDLEA, ta ce ta kama Ademola yayin da ya ke hanyar sa ta zuwa saida da kwayar a jihohin Arewacin Nijeriya.

Wani abu da ya zame wa ‘yan Nijeriya musamman a yankin Arewa annoba shi ne, ta yadda matasa da magidanta, da malamai, da ‘yan kasuwa, da direbobi kowa ya na amfani da wannan magani na A-Kurkura’.

Abin takaici kuma shi ne, maganin ya yi ajalin wasu da dama da suka fara amfani da shi, sannan likitoci sun tabbatar cewa maganin ya na cutar da lafiyar mutum, wanda sai bayan an yi shekaru ake ganin illar sa.