Home Labarai Wike Ya Ce Ba Zai Fita Daga Jam’iyyar PDP Ba

Wike Ya Ce Ba Zai Fita Daga Jam’iyyar PDP Ba

153
0

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya ce ya na nan daram a jam’iyyar PDP babu inda za shi, kuma zai cigaba da yaki domin ganin an yi abin da ya dace.

Nyesom Wike ya bayyana haka ne, a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar tare da wakilan mazabu 319 na jihar Rivers a Fatakwal, inda ya ce babu gudu ba ja da baya, ba kamar yadda ake hasashe cewa zai iya barin jam’iyyar ba.

Ya ce abin da ya sha fada wa mutane shi ne, idan akwai mai tunanin cewa za su bar PDP to ya sake tunani, amma za su yi yakin da za su yi ne a cikin jam’iyyar su.

Gwamna Wike, ya kuma yi bugun gaba da cewa duk wanda ya gudu saboda rikici a jam’iyyar sa ba jarumi ba ne, kuma abin da ba zai taba yi ba kenan.

Leave a Reply