Home Labaru Wasu ‘Yan Haɗama Ne Ke Ƙoƙarin Lalata Alaƙar Ganduje Da Tinubu –...

Wasu ‘Yan Haɗama Ne Ke Ƙoƙarin Lalata Alaƙar Ganduje Da Tinubu – Gwamnatin Kano

1
0

Gwamnatin Jihar Kano, ta gargaɗi al’umma game da yunƙurin
wasu da ta kira mamugunta kuma ‘yan haɗama, wadanda ke
yaɗa wani sautin kiran waya da aka ce na Gwamna Umar
Ganduje ne da Ibrahim Masari.

A cikin wata sanarwa da Kwamashinan Yaɗa Labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya fitar, ya ce wasu ne da aka biya su ke yunƙurin ɓata alaƙa tsakanin Ganduje da Tinubu Bola.

Ya ce a bayyane take cewa, wasu ne da ba su son ganin daɗaɗɗiyar alaƙa tsakanin Ganduje da Tinubu da kuma Masari ke amfani da wannan damar domin cimma muradun su.

Muhammad Garba ya kara da cewa, ba za su bari wasu ‘yan haɗama su lalata haɗin kai tsakanin Tunubu da Ganduje ba.