Home Labaru Wani Mutum Ya Kashe Mahaifiyarsa Kan Naira 10,000

Wani Mutum Ya Kashe Mahaifiyarsa Kan Naira 10,000

288
0

Wani mutum mai suna Osaro Owate ya shiga hannun jami’an
‘yan sanda a jihar Rivers, bisa zargin kashe mahaifiyar sa a
kauyen Alesa da ke karamar hukumar Eleme sakamakon
rashin jituwar da ta shiga tsakanin su a kan naira dubu goma
kacal.

Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa, ya na fama da matsalar gaulanci da tsatstsauran ra’ayin addini na tsawon sama da shekaru 30, ya amsa da bakin sa cewa ya kashe mahaifiyar sa da fartanya ne.

Da ya ke magana ta cikin wani faifayin bidiyo, Owate ya ce ya bukaci naira dubu ashirin ne a wajen marigayiyar tasa, domin ya sayi kayan sawa da zai yi adon zuwa wajen birne wata gawa, amma sai ta ba shi naira 10 kacal.

Ya ce ya fada mata zuwa safiyar Asabar da ta gabata ta ciro kudin da za ta ba shi, amma da su ka hadu sai ta dauko Naira dubu 10 kacal ta ba shi.

Leave a Reply