Dan takarar Gwamnan Jihar Filato a karkashin jam’iyyar APC
a zaben da ya gabata Farfesa Nentawe Yilwatda da jam’iyyar
sa, sun shaida wa kotun sauraren kararrakin zaben Jihar cewa
zababben Gwamnan Jihar Barista Caleb Mutfwang na
jam’iyyar PDP bai cancanci tsayawa takara ba.
A takardar karar da aka gabatar wa kotun, dauke da sa hannun daraktan yada Labarun dan takarar Gwamnan na APC Shitu Bamaiyi, APC ta ce Caleb bai ma cancanci ya tsaya takara a zaben ba.
Jam’iyyar APC, ta ce a lokacin da aka gudanar da zaben Gwamnan Caleb Mutfwang na jam’iyyar PDP ya saba wa dokar zabe ta kasa, don haka takarar sa haramtacciya ce.
Masu karar sun ce, a wannan takarar Caleb Mutfwang bai tsaya a karkashin jam’iyyar PDP ba, kuma bai tsaya a wata jam’iyyar ba.














































