Home Home Umarnin Kotu: Ba Mu Hana Emefiele Ganin Iyali Da Lauyoyinsa Ba –...

Umarnin Kotu: Ba Mu Hana Emefiele Ganin Iyali Da Lauyoyinsa Ba – DSS

77
0

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta ce an ba tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele damar ganin iyalin sa da likitocin sa tun kafin kotu ta bada umarni.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja dai ta ba hukumar  DSS umarnin ta ƙyale Emefiele ya gana da iyalai da lauyoyin sa, sai dai a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bakin kakakin ta Peter Afunanya, hukumar ta ce ta riga ta ba Emefiele damar yin haka tun kafin kotu ta bada umarni.

Sanarwar ta ƙara da cewa, hukumar DSS ta na yin abin da ya dace wajen kula da sha’anin bincike da duk wani da ake zargi da ke ƙarƙashin kulawar ta, kuma ta na aiki da ƙwarewa da martaba doka daidai da tsarin mulkin dimokuraɗiyya.

Hukumar DSS, ta kuma gargaɗi masu take-taken yaƙi da binciken da ake yi wa Godwin Emefiele su yi taka-tsa-tsan.

Leave a Reply