Home Labaru Uba Sani Ya Kafa Kwamitin Tsara Yadda Za A Kyautata Wa Ma’Aikatan...

Uba Sani Ya Kafa Kwamitin Tsara Yadda Za A Kyautata Wa Ma’Aikatan Kaduna

86
0

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, ya ce zai maido
kyakkyawar alakar da ke tsakanin gwamnatin jihar da
kungiyar Kwadago.

A wani taro da gwamnan ya yi da kungiyar kwadago domin samun maslaha da kuma tattauna yadda kungiyar da gwamnati za su yi aiki tare domin samun kyakkyawar fahimta a tsakanin
su, gwamna Uba Sani ya ce zai warware matsalolin da ma’aikatan jihar Kaduna ke fama da su nan ba da dadewa ba.

Gwamnatin jihar Kaduna dai ta kafa kwamiti kwamitin da zaitsara yadda za a kyautata wa ma’aikatan jihar a ƙarkashin jagorancin mataimakiyar gwamnan Hadiza Balarabe, wanda zai zauna da wakilan kungiyar kwadago domin tattauna yadda alakar gwamnati da ma’aikata za ta kasance cikin aminci da fahimtar juna.

Daga cikin abubuwan da kwamitin zai duba akwai yadda gwamnati za ta tallafa wa ma’aikata domin rage raɗaɗin cire tallafin mai da aka yi, wanda ya sa farashin abubuwa ya yi tashin gwauron zabo.

Leave a Reply