Home Labaru Tsohon Gwamnan Binuwai, Samuel Ottom Ya Amsa Gayyatar EFCC

Tsohon Gwamnan Binuwai, Samuel Ottom Ya Amsa Gayyatar EFCC

281
0

Tsohon Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom, ya amsa
gayyatar Hukumar Yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC.

Hukumar EFCC dai ta gayyaci tsohon gwamnan ne domin ya amsa tambayoyi a kan abin da ya shafi zamanin mulkin sa.

Rahotananni sun ce, Samuel Ortom ya isa harabar ofishin hukumar da ke Makurdi ne da misalin ƙarfe 10: na safe.

Ana dai tunanin hukumar EFCC ta na tuhumar tsohon gwamnan ne da zargin tafka rashawa lokacin da ya ke kan karagar mulki.

Leave a Reply