Home Labarai Tsaro Ya Inganta a Mulkin Buhari – Fadar Shugaban Ƙasa

Tsaro Ya Inganta a Mulkin Buhari – Fadar Shugaban Ƙasa

1
0

Fadar shugaban ƙasa, ta ce shugaba Buhari zai bar mulki
yayin da harkar tsaro da tattalin arzikin Nijeriya su ka inganta
fiye da yadda ya same su a shekara ta 2015.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Femi Adesina ya bayyana haka, yayin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels.

Masu suka dais u na zargin cewa, harkar tsaron Nijeriya ta taɓarɓare a ƙarƙashin mulkin shugaba Buhari, sakamakon zargin sa da son kai wajen naɗe-naɗen muƙamai musamman na tsaro maimakon duba cancanta ko tsarin raba-daidai na muƙaman tarraya.

Sai dai Adesina ya kare matakin da cewa, ana yin naɗin muƙaman manyan hafsoshin tsaron Nijeriya ne bisa cancanta, domin bai kamata a siyasantar da harkar tsaro wajen naɗin muƙamai ba.

Femi Adesina, ya ce ko ma menene mutane za su ce, Buhari zai bar mulkin Nijeriya a daidai lokacin da ƙasar nan ta inganta fiye da yadda ya same ta a shekara ta 2015.