Home Labaru Tsaro: Sojoji Sun Kama Mai Saida Wa Boko Haram Kayan Aiki A...

Tsaro: Sojoji Sun Kama Mai Saida Wa Boko Haram Kayan Aiki A Hanyar Baga

459
0

A ranar Lahadin da ta gabata ne, aka bayyana kama wani da ake zargin ya na saida wa mayakan Boko Haram kayayyakin masarufi a Jihar Borno.

Kwamandan Rundunar ta 7 AK Ibrahim ya gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a Sansanin Gubio na Musamman da ke Maiduguri.

An dai kama wanda ake zargin da tsofaffin tayoyin babura guda 136, dankon gam na facin taya.

AK Ibrahim, ya ce an kama Samuel Chukwudon ne a kan hanyar Baga zuwa Munguno a cikin motar sa, kuma an tabbatar hanyar Tafkin Chadi ya dosa, inda Boko Haram su ka yi kaka-gida su na amfani da Babura wajen kai hare-hare.

Sai dai Chukudon ya shaida wa manema labarai cewa shi ba Boko Haram ya ke saida wa kaya ba, ya na mai cewa shi mazaunin garin Monguno ne tun a shekara ta 1990, kuma ya na saida wa masu kurar saida ruwa tsofaffin tayoyin babura ne ba ‘yan Boko haram ba.