Gagararren shugaban kungiyoyin ta’addancin da su ka addabi yankunan jihohin Benue da Nasarawa da Taraba Leggi Jibrin ya shiga hannun jami’an tsaro, bayan artabun musayar wuta da ya yi da dakarun sojin rundunar Operation Whirl Stroke da rundunar tsaro ta hadin gwiwa da ke kula da jihohin uku.
Wata majiyar tsaro ta ce, dan bindigar ya shiga hannun sojoji ne a kauyen Agam da ke karamar hukumar Nasarawa yayin da su ka fita aiki.
Majiyar ta ce, dakarun sun yi aikin ne a ranakun Laraba da Alhamis a karkashin umarnin kwamandan rundunar Manjo Janar Kevin Aligbe, lamarin da ya yi sanadiyyar ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Toto.
Ta ce wasu daga cikin abubuwan da aka samu daga ‘yan bindigar, sun hada da bindiga kirar AK-47, da samfurin AK-49 da harsasai masu rai 106, da kuma wayar tafi da gidan ka.