Harin da ‘yan kungiyar rajin kafa kasar Biafra su ka kai wa Sanata Ike Ekweremadu a kasar Jamus babban laifi ne kuma ta’addanci ne kamar yadda Jakadan Nijeriya ya bayyana, tare da kalubalantar ‘yan sandan kasar Jamus su gaggauta gurfanar da su domin su fuskanci hukunci.
Sai dai ‘yan sandan kasar sun ce, kawai masu zanga-zanga ne kimanin su 30 su ka yi wa Ekweremadu zanga-zanga, daga nan kuma su jami’an tsaron su ka yayyafa wa wutar rikicin ruwa.
Jakadan Nijeriya a kasar Jamus Yusuf Tuggar, ya ce ba dalili ba ne ‘yan sanda su kira abin da aka yi wa Ekweremadu da sunan zanga-zanga.
Shugaban kungiyar Nnamdi Kanu ya dauki alhakin cewa su ne su ka kai wa Ekwerumadu harin, kuma a haka za su ci gaba da tozarta shugabannin Inyamirai a kasashen waje.
Jakada Yusuf Tuggar, ya ce su na jira su ga abin da mahukuntan kasar Jamus za su yi da kuma matakin da za su dauka a kan wannan mummunan lamari.