Home Labaru Tinubu Ya Sa Hannu Kan Dokar Tsawaita Aikin Alƙalai Zuwa Shekaru 70

Tinubu Ya Sa Hannu Kan Dokar Tsawaita Aikin Alƙalai Zuwa Shekaru 70

303
0

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sa hannu a kan
ƙudirin dokar da ke neman tsawaita wa’adin ritayar alkalan
babbar kotun tarayya daga shekaru 65 zuwa 70.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙasa Abiodun Oladunjoye ya fitar, ya ce Tinubu ya sanya hannu a kan dokar da Majalisar tarayya mai barin gado ta gabatar.

Tare da sanya hannu a kan dokar gyaran kundin tsarin mulki, shekarun ritayar jami’an shari’a da haƙƙin fansho sun kasance an daidaita su da sauran batutuwa masu alaƙa.

Yayin da ya ke sanya hannu a kan ƙudirin dokar, Tinubu ya yi alƙawarin cewa gwamnatin shi za ta jajirce wajen ƙarfafa ɓangaren shari’a da tabbatar da bin doka da oda, tare da ba jami’an shari’a damar gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Leave a Reply