Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da majalisar tattalin arziki ta kasa.
An dai kaddamar da majalisar ne a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima.
A wani saƙo da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Dada Olusegun ya wallafa a shafin sa na twitter, ya ce an ƙaddamar da majalisar ne a zauren ta da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja.
Ƙwarya-ƙwaryar bikin ya samu halartar shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, da Sakataren Gwamnatin tarayya Sanata George Akume tare da gwamnonin jihohin Nijeriya 36.
Yayin ƙaddamar da majalisar, Shugba Tinubu ya shawarci gwamnonin su haɗa kai wajen bunƙasa ƙananan hukumomi da ababen more rayuwa, duba da manyan ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta.