Home Labaru Tinubu Na Neman Sahalewar Majalisar Wakilai Don Samar Da Kudaden Rage Radadi

Tinubu Na Neman Sahalewar Majalisar Wakilai Don Samar Da Kudaden Rage Radadi

89
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya rubuta wa majalisar
wakilai wasikar neman gyara a kwarya-kwartar kasafin kudin
shekara ta 2022, domin samun amincewar daukar Naira
biliyan 500 da nufin rage wa ‘yan Nijeriya radadin cire
tallafin man Fetur.

Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ne ya karanta wasikar shugaba Tinubu a zauren majalisar, inda ya ce bukatar ta zama dole domin a ba gwamnati damar rage wa ‘yan Nijeriya radadin cire tallafin man fetur.

A cikin wasikar, Shugaba Tinu ya ce ya rubuta ne don neman a yi wa dokar karin kasafin kudin shekara ta 2022 kwaskwarima, lamarin da ya ce ya zama dole domin samar da
kudade da abubuwan da su ka dace don a rage radadin cire tallafin man fetur ga ‘yan Nijeriya.

Wasikar ta ce ana bukatar a ciro Naira biliyan 500 daga cikin karin kasafin kudin shekara ta 2022, domin samar da kayan tallafi ga ‘yan Nijeriya sakamakon cire tallafin fetur da aka yi.

Shuga Tinubu ya bukaci majalisar cikin ​gaugawa ta yi la’akari da bukatar hakan don a ba gwamnatin sa damar samar da abubuwan jin kai ga ‘yan Nijeriya.

Leave a Reply