Home Labarai Teburin Firimiya: Arsenal Ta Karbi Jagoranci Bayan Nasara Kan Luton

Teburin Firimiya: Arsenal Ta Karbi Jagoranci Bayan Nasara Kan Luton

46
0

Arsenal ta koma jagorancin teburin Firimiyar Ingila bayan nasarar doke Luton da kwallo 2 da nema a daren jiya Laraba, ko da ya ke haduwar Liverpool da Shiffield United ce za ta tabbatar da ci gaba da zaman tawagar ta Mikel Arteta a saman teburin ko akasin haka.

Arsenal ta doka wasan na jiya ne ba tare da dan wasanta mafi zura kwallo ba, wato Bukayo Saka wanda ya samu rauni yayin haduwar su da Manchester City a karshen mako.

Yanzu haka Arsenal na jagoranci ne da maki 68 tazarar maki guda tal tsakaninta da Liverpool a gurbin ta biyu da kuma Manchester City a gurbin ta 3, ko da ya ke tawagar Jurgen Klopp na da wasa guda a hannu.

Luton FC ta doka wasan na jiya ne tare da tarin ‘yan wasanta ba, wanda ya tilasta mata dauko kananun ‘yan wasa daga kwalejin horar da ‘yan wasa na kungiyar.

Leave a Reply