Home Labaru Kiwon Lafiya Tashin Gobara: An Shawarci Gwamnati Ta Samar Da Cibiyoyin Kashe Gobara A...

Tashin Gobara: An Shawarci Gwamnati Ta Samar Da Cibiyoyin Kashe Gobara A Fadin Nijeriya

238
0

Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara Abdulwaheed
Yakub ya roki gwamnatin tarayya ta kafa cibiyoyin kashe
gobara irin na zamani a kowace karamar hukuma da ke fadin
Nijeriya.
Yakub ya yi wannan rokon ne a lokacin wata tattaunawa da ya
yi da kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN a Ilorin, inda ya
kara da cewa, samar da cibiyoyin kashe gobarar zai taimaka
wajen kare rayuka da dukiyoyi a duk lokacin da bukatar hakan
ta taso.

A cewar sa, rayuka masu yawa da mahimman dukiyoyi aka yi
asarar su, a gobara da aka samu a wuraren da babu cibiyoyin
kashe gobarar, saboda haka ya ce shawartar gwamnatin tarayya
ta hada kai da gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki
a kan harkokin kashe gobara domin ganin an kakkafa cibiyoyin
kashe gobarar a ko’ina a Nijeriya.
Yakubu ya shawarci ‘yan Nijeriya su rungumi dabi’ar hana
tashin gobara domin kare rayukan su da dukiyoyin su.