Home Labaru Taron ECOWAS: Shugaba Buhari Ya Yi Magana Game Da Barazanar ‘Yan Ta’adda...

Taron ECOWAS: Shugaba Buhari Ya Yi Magana Game Da Barazanar ‘Yan Ta’adda A Duniya

361
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga shugabannin kasashen Afrika wajen taron kungiyar bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen afrika ta yamma wato ECOWAS su tashi tsaye wajen yaki da ta’addanci a Nahiyar.

Shugaban kasa ya nemi takwarorinsa shugabanni su dage wajen ganin ‘yan ta’adda ba su rikita yankin Afrika ba, saboda dole ayi kokari wajen ganin jama’a sun zauna lafiya cikin aminci.

Buhari, ya yi wannan kiran ne a jawabinsa wajen babban taron na ECOWAS da aka shirya domin ganin gwamnatoci da shugabanni sun ga karshen ta’addanci da ya addabi jama’a.

Shugabannnin kasashe irinsu Chadi da Mauritania sun halarci wannan taro na kwana guda, inda shugaban Najeriya Buhari ya ja masu kunnen cewa ‘yan ta’adda su na neman zama barazana a Afrika da ma fadin Duniya,  don haka ya zama nauyi a kan su. Ya cewa yawan hare-haren da ‘yan ta’adda suke kai wa, da kuma irin manyan makaman da suke samu, abin tada hankali ne ga al’ummar Afrika.