Home Labaru Tallafi: An Ware Wa Zamfara Naira Biliyan 10 A Kasafin Shekara Ta...

Tallafi: An Ware Wa Zamfara Naira Biliyan 10 A Kasafin Shekara Ta 2019

301
0

Majalisar dokoki ta tarayya, ta kebe wa jihar Zamfara naira biliyan 10 a kasafin shekara ta 2019, domin inganta rayuwar al’ummar yankin, musamman yara marayu da matan da mazajen su su ka mutu.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin da hare-haren ‘yan bindiga da masu satar mutane da barayin shanu ke neman durkusar da tattalin arzikin ta.

Mutane da dama ne su ka rasa rayukan su, yayin da yara da dama su ka kasance marayu sakamakon kashe-kashen da ke faruwa a jihar.

Sanata Kabiru Marafa ya ce sun yi farin ciki da hakan, kuma kudin za su taimaka wa yankin daga fadawa wata masifa, sannan ya bukaci fadar shugaban kasa ta kafa wani kwamiti domin maganin wadannan matsaloli.

Leave a Reply