Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Kungiyar Asiri Sun Halaka Wani Basarake A Jihar Delta

Ta’addanci: ‘Yan Kungiyar Asiri Sun Halaka Wani Basarake A Jihar Delta

287
0

Duk da dokar hana yawo da aka saka a karamar hukumar Udu ta jihar Delta don kawo karshen kungiyoyin asirin da suke baje kolinsu a yankin, an samu rahoton kashe wani basarake mai suna Egolor Kolo.

An kashe basaraken Dan yaren Urhobo a ranar Alhamis a Ukpiovwin cikin garin Udu da karfe 8:00 na yamma.

 “Fada mai tsanani ya tashi Inda har aka kai ga sokawa mamacin wuka duk da dokar ta bacin da aka sanya,” inji jaridar TribuneOnline.

Wani babban jami’in ‘yan sandan Najeriya ya sanar da jaridar TribuneOnline cewa salon cajen da jami’an tsaro ke yi don zakulo ‘yan kungiyar asiri a karamar hukumar ba zai yi aiki ba.

Ya ba jami’an tsaro shawarar su je har gidajen ‘yan kungiyar asirin ne don zakulo su. Tsayawa kan titina tare da caje ba zai kawo karshen matsalar ba.

Idan zamu tuna, shugaban karamar hukumar Udu, Jite Brown, a makon da ya gabata ya sanya dokar ta baci a karamar hukumar don kawo karshen fadace-fadacen ‘yan kungiyar asiri a yankin. Yankunan da dokar ta bacin ta shafa sun hada da birnin Ovwia, Ekete cikin gari, Ekete ta yankin ruwa, birnin Owhase, Orhuwhorun junction, Express Junction da Mofor Junction.