Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Kasuwa Tare Da Ƙona Motar ‘Yan...

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Kasuwa Tare Da Ƙona Motar ‘Yan Sanda A Jihar Kano

272
0

Wasu ‘yan bindiga sun sace wani ɗan kasuwa tare da ƙone motar ‘yan sanda a garin Minjibir da ke jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa, bindigar sun kai harin ne a daren Talatar da ta gabata, inda su ka shiga gidajen maƙwaftan mutumin kafin daga bisani su yi awon gaba shi.

Wannan dai ya na zuwa ne, ƙasa da kwanaki huɗu bayan masu garkuwa da mutane sun sace wata mata da ɗan da ta ke raino a garin Falgore na Ƙaramar Hukumar Rogo da ke maƙwaftaka da jihohin Kaduna da Katsina.

Wani mazaunin garin Minjibir da abin ya faru a kan idon sa, ya ce bayan ‘yan bindigar sun isa garin, sai da su ka fara shiga gidajen mutane su na neman attajirin, sannan daga bisani su ka ɗauke shi a gidan sa.

Wata majiya ta ce, ‘yan sanda daga sassa daban-daban na jihar Kano sun kai ɗauki a lokacin da lamarin ke faruwa, inda su ka yi ba-ta-kashi da ‘yan bindigar, amma ‘yan bindigar sun samu nasarar ƙona motar ‘yan sandan ɗaya bayan sun buɗe mata wuta.