Home Labaru Ta’addanci: Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 23 A Katsina

Ta’addanci: Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 23 A Katsina

408
0

Wani harin ‘yan bindiga ya hallaka sojan Najeriya 23 a kauyen Shimfida na karamar hukumar Jibiya ta jihar, Katsina, yankin da ke fama da tashe-tashen hankula na ‘yan bindiga da masu garkuwa da jama’a.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito wani hafsan sojan Najeriya na cewa har yanzu da akwai wasu sojojin da dama wadanda harin ya rutsa da su da ba a ji duriyarsu ba, baya ga wadanda aka hakikance sun hallaka.

Wani dan kato da gora ya shedawa manema labarai cewa har zuwa yammacin ranar Lahadi ana ci gaba da neman sauran sojan da suka bata, inda ya nuna fargabar ko adadin sojojin da suka gamu da ajalin su ka iya karuwa.

Daga cikin dakarun da suka riga mu gidan gaskiya sun hada da masu mukamin Manjo, Kyaftin, da Laftanar.

Sai dai yayin da aka tuntubi kakakin rundunar sojin kasa, Kanal Sagir Musa, ya ce ba zai iya bayar da tabbaci ba, kuma ba ya da ta cewa domin lokacin shi ne karo na farko da ya sami labarin harin.