Home Labaru Ta’addanci: Mun Kammala Bincike Kan Fasa Kurkukun Kuje — Aregbesola

Ta’addanci: Mun Kammala Bincike Kan Fasa Kurkukun Kuje — Aregbesola

30
0

Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola, ya bayyana cewar gwamnatin tarayya ta kammala bincike tsaf kan fasa gidan gyaran hali na Kuje da ke nan birnin Abuja,

Ya ce koda yake an kama wasu daga cikin tserarrun fursunonin da dama, har yanzu wadanda suka gudun na da matukar yawa.

A ranar biyar ga watan Yulin bana ce dai wasu ’yan ta’adda suka fasa gidan yarin na Kuje da ke Abuja, inda akasarin fursunonin gidan, ciki har da dukkan ’yan Boko Haram din da ake tsare da su a ciki, suka tsere.

Aregbesola ya bayyana haka ne yayin jawabi ga ’yan jarida karo na hudu kan nasarorin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ma’aikatarsa.

Ya kara da cewar akwai matakai daban-daban na bincike, kuma ma’aikatar harkokin cikin gida ta kamala nata bangaren inda ta tura rahotonta, amma kasancewar abu ne da ya shafi tsaro, ba zai yiwu a bayyana komai ba a nan.