Taƙaddama ta ƙaure tsakanin gwamnatin APC da jam’iyyar
PDP a jihar Zamfara, bayan an yi zargin cewa ƙananan
kwamitocin karɓar mulki na gwamati mai jiran gado su na
wuce gona da iri.
Gwamnatin jihar Zamfara dai ta yi zargin cewa, ƙananan kwamitocin su na zuwa ma’aikatun gwamnati su na yin bincike tare da karɓar bayanai, wanda a cewar ta abu ne da bai dace ba kuma ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki.
Ta ce abubuwan da kwamitocin ke yi tamkar kafa gwamnati ne a cikin wata gwamnati, inda ta buƙaci su jira har sai an miƙa masu mulki.
Kwamishinan yaɗa labara na jihar Zamfara Ibrahim Dosara, ya ce ƙananan kwamitocin sun kasance su na bin ma’aikatu su na karɓar bayanai da gudanar da bincike tare da karɓar bayanan asusun ajiya na ma’aikatun domin yin bincike.














































