Tsohon gwamman jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman
Bakura, ya ce zama teburin sulhu da ‘yan bindiga ne hanyar
da ta fi dacewa domin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta
addabi yankin arewa maso yammacin Nijeriya.
Ya ce irin zama teburin sulhu da gwamnatin tarayya ta yi da ‘yan Neja Delta, idan aka bi irin tsarin za a iya shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma.
Yariman Bakura, ya yi kira ga sabbin manyan hafsashin tsaro su zauna da ‘yan bindigar kamar yadda a baya aka zauna da tsagerun yankin Naija Delta a fara maganar sulhu da su.
Tsohon gwamnan ya cigaba da cewa, idan hakan ta gagara sai a bi su duk inda su ke a ɗauki matakin da ya dace.
Ya ce ba wai zama da su a yi masu alƙawari sannan a watse ne sulhu ba, domin ya bibiyi duk sulhun da aka yi da su a baya, amma duk alƙawuran da aka yi masu an saɓa, domin ba za ka kira mutumin da talauci da jahilci su ka sanya shi shiga daji sannan ka yi tunanin yin sulhu da shi ba tare da ka cika ma shi alƙawuran da ka ɗauka ba.