Home Labaru Sufuri: Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Zai Fara Aiki Kafin Babbar Sallah – Amaechi

Sufuri: Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Zai Fara Aiki Kafin Babbar Sallah – Amaechi

258
0

Ministan sufuri Rotimi Ameachi, ya ce za a cigaba da jigilar fasinjoji da jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja kafin Babbar Sallah.

A ranar Asabar din nan ne ake sa ran gudanar da gwajin sabbin jiragen ƙasan da aka kawo Kaduna, sai dai za a fara amfani da su ne idan an cigaba da jigilar. Ministan, ya buƙaci hukumar gudanarwa ta jirgin ƙasa ta Niajeriya ta ɗauki matakan daƙile yaɗuwar korona kafin buɗe jigilar jiragen.