Home Labarai Sojojin Sama Sun Hallaka Yan Bindiga Da Dama A Kaduna Da Zamfara

Sojojin Sama Sun Hallaka Yan Bindiga Da Dama A Kaduna Da Zamfara

261
0
Troops Zamfara
Troops Zamfara

Hare-haren da dakarun sojin saman Nijeriya, suka kaddamar sun kashe gomman ‘yan bindiga a jihohin Kaduna da Zamfara, tare da kuma lalata matatun danyen mai 25 a jihohin Imo da Ribas.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Edward Gabkwet ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

Ya ce rundunar ta Operation Whirl Punch ta ci gaba da aikinta na gano sansanin ‘yan bindiga tare da kawo karshensu.

Ya ce bayanan sirri sun nuna cewa ‘yan bindigar da ke addabar al’umma a karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja suna zaune ne a Jihar Kaduna.

A cewarsa, karin bayanan sirri sun nuna cewa wadannan ‘yan bindigar suna yin balaguro daga dajin Allawa na Jihar Neja zuwa dajin Malum na karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

 A yankin Neja Delta kuwa, Gabkwet, ya ce dakarun karkashin rundunar musamman ta Operation Delta Safe sun lalata haramtattun matatun danyen mai har guda 25 a yankin Ohaji/Egbema.

Leave a Reply