Home Labarai Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno

Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno

118
0

Rahotanni na cewa, dakarun soji a karamar hukumar Bama ta Jihar Borno sun kashe mayakan Boko Haram shida a wani samame da su ka kai wata kasuwa ta haramtacciyar hanya da ‘yan ta’addan su ka kafa.

Sojojin tare da hadin gwiwar rundunar sa-kai ta CJTF, sun kai farmaki a kan haramtacciyar kasuwar da aka fi sani da Kasuwar Daula a kauyen Bararam da ke garin Bama.

Wani masani a kan yaki da ta’addanci kuma mai sharhi a kan harkokin tsaro a tafkin Chadi Zagazola Makama, ya ce ‘yan ta’addan sun bude wuta ne bayan sun ga sojojin, inda a nan ne sojojin su ka kashe shida daga cikin su.

A cewar sa, a kasuwar ana saida wa ‘yan ta’addan kayayyaki irin su masara da wake da gishiri da kwayoyi da kuma man fetur.

Ya ce sun kama wasu da dama daga cikin mayakan Boko Haram da su ka hada da masu samar da kayan aiki da masu hada kai wajen hada makamai.