Home Home Sojoji Sun Halaka Gawurtattun Shugabannin Yan Bindiga Ado Aliero Da Dankarami A...

Sojoji Sun Halaka Gawurtattun Shugabannin Yan Bindiga Ado Aliero Da Dankarami A Zamfara

89
0

Rundunar sojin sama ta Nijeriya, ta hallaka jiga-jigan ‘yan bindiga biyu da su ka hada da Ado Aliero da Dankaram yayin luguden wuta daga sama a jihar Zamfara.

Yayin luguden wutar, rundunar sojin ta yi nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga 10 da suka addabi yankunan Arewa maso Yamma.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jami’an ta sun kara kaimi wajen kakkabe ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, a kokarin ta na kakkabe ‘yan bindiga da ayyukan su a yankin Arewa maso Yamma, rundunar ta kara kaimi a wani samame da ta kai tsakanin ranakun 28 zuwa 29 ga watan Yuli.

Kakakin rundunar sojin saman Edward Gabkwet ya shaida wa manema labarai cewa, babban hafsan sojin sama Air Marshal Hassan Abubakar ya umarci a cigaba da kakkabe ‘yan bindigar da su ka addabi yankin.

Leave a Reply